Isa ga babban shafi
Libya

Majalisar Dinkin Duniya za ta gudanar da taron gaggawa kan Libya

Yau Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani taron gaggawa kan halin da ake ciki a kasar Libya, bayan da Khalifa Haftar ya umurci dakarun sa da su kutsa kai birnin Tripoli domin karbe iko.

Khalifa Haftar da Fayez Al Sarraj na kasar Libya
Khalifa Haftar da Fayez Al Sarraj na kasar Libya FETHI BELAID, KHALIL MAZRAAWI / AFP
Talla

A wani jawabi da yayi ta faifan bidiyo, Haftar yace lokaci yayi, inda yayi alkawarin kare fararen hula da hukumomin gwamnati.

Birtaniya ta bukaci gudanar da taron, yayin da Amurka da Faransa da Italiya da Daular Larabawa da kuma kungiyar kasashen Turai suka bukaci taka can can daga kowane bangare.

Rahotanni sun ce yanzu haka dakarun Haftar na gaf da isa Tripoli, yayin da dakarun Fayez al-Sarraj yace ya baiwa dakarun sa umurnin magance duk wata barazana.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres wanda ya ziyarci kasar ya bayyana cewar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.