Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano

Kotu ta dakatar da shirin gwamnatin Kano na karin masarautu 4

A Najeriya, wata babbar kotu a Kano da ke zamanta a Ungoggo, ta bada umarnin dakatar da shirin Gwamnatin jihar, na karin masarautu 4, zuwa masu daraja ta 1 a Jihar.

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi na biyu
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi na biyu Reuters
Talla

Kafin umarnin kotun dai a yau Asabar ne gwamnan jihar Abdullahi Ganduje, ke shirin bikin nadin sabbin Sarakunan 4 a masarautun da suka hada da Rano, Bichi, Gaya da kuma Karaye.

Yayin zaman shari’ar a jiya Juma’a, mai shari’a Nasiru Saminu, da ya yanke hukuncin ya kuma bada umarnin dakatar da buga takardun da ke bayyana dokar da ta bada damar daga darajar Karin masarautun guda 4.

Alkalin ya tsayar da 15 ga watan Mayu da muke ciki a matsayin ranar da zai ci gaba da sauraron shari’ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.