Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

Matasa sun yi wa masu garkuwa da mutane kofar rago

Daruruwan mutane sun datse manyan hanyoyin Kaduna zuwa Abuja da kuma Kaduna zuwa Zaria, inda suke gudanar da zanga-zangar nuna bacin rai kan yadda wani mutum ya rasa ransa, bayan da harsashin da jami’an ‘yan sanda suka harba ya same shi.

Wasu 'Yan sandan Najeriya
Wasu 'Yan sandan Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Rahotanni sun ce lamarin ya samo asali ne da safiyar Yau Litinin, bayan da mazauna unguwar Kawo a Kaduna suka samu labarin cewa wasu masu garkuwa da mutane uku na kokarin sace wasu mazauna yankin.

Jin labarin ya sa jama’a datse hanyoyin shiga unguwar, zalika su ka kurewa masu garkuwa da mutanen gudu har suka yi nasarar kama guda tare da kone shi nan take.

Rahotanni daga jihar Kadunan sun ce jami’an tsaro sun yi gaugawar isa wurin da lamarin ya auku domin maido da doka da oda.

Bayan isarsu wajen suka soma harbi cikin iska da nufin tarwatsa jama’ar da suka yi dandanzo, amma hakan ya yi sanadin jikkatar wasu mutane 4, daya daga cikinsu kuma ya rasa ransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.