Isa ga babban shafi
Sudan

Sudan: Sojoji sun soke yarjejeniyar da suka cimma da fararen hula

Sojoji da ke kan karagar mulkin kasar Sudan sun sanar da soke yarjejeniyar raba madafun iko da kuma kafa gwamnatin hadin gwiwa da fararen hula, wadda a baya suka cimma matsaya akai, tsakaninsu da shugabannin masu zanga-zanga.

Shugaban majalisar mulkin sojin kasar Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan.
Shugaban majalisar mulkin sojin kasar Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan. AFP
Talla

Matakin na kunshe ne, a jawabin da shugaban majalisar mulkin sojin kasar ya gabatar a daren ranar litinin, bayan da sojojin suka yi amfani da karfi don kawo karshen tarzomar da ake yi a kasar.

Shugaban majalisar mulkin sojin na Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya ce bayan soke yarjejeniyar da aka kulla tsakanin bangarorin biyu, za gudanar da zabukan kafa sabuwar gwamnatin farar hula a cikin watanni 9 masu zuwa a kasar.

Wannan dai mataki ne da shugaban ya sanar sa-o-i kadan bayan da sojoji suka bude wuta a kan daruruwan mutane da ke zaman dirshen a harabar ginin ma’aikatar tsaron kasar, inda sabbin alkalumma suka tabbatar da cewa an kashe akalla mutane 35, yayin da wasu sama da 100 suka samu raunuka.

A yau dai an wayi gari ba tare da wani tashin hankali ko kuma zanga-zanga a cikin birnin na Khartoum ba, yayin da al’ummar kasar suka fita domin gudanar da bukukuwan sallah a cikin yanayi na juyayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.