Isa ga babban shafi
Afrika

An kama wasu yan Najeriya bisa laifin garkuwa da mutane a Ghana

Yan Sanda a kasar Ghana sun sanar da kama wasu yan Najeriya guda 3 cikin mutanen da ake zargi da sace wasu yan kasar Canada guda biyu da aka yi garkuwa dasu a baya.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo lokacin da aka rantsar da shi a Accra
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo lokacin da aka rantsar da shi a Accra
Talla

Wannan dai ba shine karo na farko da ake kama yan Najeriya da aikata irin wannan laifi a kasar ta Ghana, Kazalika a watan Afrilun da ya gabata, an sace wani dan kasar India a birnin Kumasi, wanda aka nemi makudan kudade kafin sakin sa, sai dai ba a dauki lokaci mai tsawo ba jami’an tsaron kasar suka yi nasarar ceto shi.

Wata kdiddiga ta nuna cewa, a duk shekara sama da ‘yan kasashen ketare miliyan daya da dubu 300 ne ke ziyartar kasar Ghana, akasarinsu domin yawan shakatawa da kuma kasuwanci.

Ambassada Ibrahim Kazaure, tsohon Jakadan Najeriya a Saudi Arabia, ya bayyana damuwa kan yadda matsalar ke iya shafar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.