Mayakan Boko Haram sun yiwa dakarun Chadi kwanton Bauna
Akalla sojojin Chadi 7 tare da wani mai gadi ake zaton sun mutu sakamakon wani kazamin hari da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai kusa da tafkin Chadi, bayan sun yiwa sojojin kwanton Bauna.
Wallafawa ranar:
Majiyar tsaro tace an kashe sojojin ne ranar Juma’ar da ta gabata a Mbomouga dake Yankin Ngouboua a kasar ta Chadi, yayin da wasu mutane 13 suka jikkata.
Rahotanni sun ce cikin sojojin da aka kasha har da mai rike da mukamin Kanal, yayin da wata majiya ta daban tace manyan hafsoshi 3 suka mutu.
A watan Maris da ya gabata, sojojin Chadi 23 mayakan suka kashe a hari mafi muni da aka gani.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu