Isa ga babban shafi

Kamaru ta fara zaman warware rikicin 'yan aware

Gwamnatin Kamaru ta bude wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki don lalubo hanyoyin warware rikicin yankin ‘yan aware masu amfani da turancin Ingilishi wanda ke barazanar tsaro ga kasar baya ga hallaka daruruwan jama’a.

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya REUTERS/Mike Segar
Talla

Da safiyar yau Litinin ne, gwamnatin Kamaru ta bude zaman tattaunawar wadda ta fara gudana a fadarta da ke Yaounde babban birnin kasar, zaman da zai kunshi hatta wakilcin jagororin ‘yan awaren baya ga sauran masu ruwa da tsaki a kasar.

Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa AFP da ke wajen tattaunawar, ya bayyana cewa zaman ya kankama ne bayan jawabin Firaministan Kamaru Joseph Dion kuma ana sauran zaman ya ci gaba da gudana har zuwa ranar 4 ga watan Agusta mai kamawa.

Cikin Kalaman shugaba Paul Biya da ya jagoranci kasar har na tsawon shekaru 37, ya ce yana fatan tattaunawar ta kawo karshen rikicin ‘yan awaren.

Sai dai tun gabanin fara zaman tattaunawar, akwai hasashen gaza iya samun nasara la’akari da yadda gwamnatin Paul Biya ta kame tarin masu fafutuka baya ga wasu shugabannin ‘yan awaren.

Tun bayan fara rikicin ‘yan awaren na Kamaru da ke kokarin kafa kasa mai cin gashin kanta a shekarar 2017 akalla mutane dubu 3 suka mutu yayinda fiye da rabin miliyan suka gudu daga muhallansu don neman mafaka a kasashen makwabta.

Bangaren ‘yan awaren da ake bayyana yawansu da akalla kashi 5 na al’ummar kamaru mai yawan jama’a miliyan 24 akwai zarge-zargen da ke nuna basa samun daidaito da sauran ‘yan kasar da ke amfani da turancin Ingilishi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.