Isa ga babban shafi

Faransa na gayyatar aminanta don tura dakarun su yankin Sahel

Faransa na kokarin shawo kan kasashe aminata domin su tura dakarun musamman zuwa yankin sahel, don taimakawa sojojin Mali yakar ‘yan ta’addanci da ya addabi yankin.Yunkurin na Faransa na zuwa ne bayan da kwanakin da suka gabata wani gungun mayaka masu ikirarin jihadi suka halaka sojojin Mali 25.

Dakarun tsaron Mali cikin aikin sintiri na ayyukan G5 sahel
Dakarun tsaron Mali cikin aikin sintiri na ayyukan G5 sahel Daphné BENOIT / AFP
Talla

A cewar Faransa da sojojinta ke yankin sahel tun a shekarar 2013 matsalar nada girma, kara zage dantse ga dakarun Mali da Jamhuriyar Nijer da kuma Burkina faso kadai ne zai iya dakile barazanar a daidai wannan lokaci da kasar ta fara shirin tsame hannun sojojinta daga cikin rikicin.

manufar tsoma hannun sojojin Faransa a rikicin na Mali manufofi ne guda biyu, kamar yadda shugaban rundunar sojan faransa janar François Lecointre ya sanar a watan Yunin da ya gabata cewa: ta farko ita ce rage karfin mayakan na jihadin, ta yadda za su kasance masu rauni a gaban sojin na Mali,ta yadda zasu iya tunkararsu su kadai, ko kuma tare da dan kankanin taimako, dakarun a rundunar yaki da 'yan ta’adda na kasar Faransa Barkhane.

Duk da horon da a wani lokaci can baya kungiyar tarayyar turai da rundunar Barkhane, suka baiwa sojojin na kasar Mali, har yau sun ci gaba da zama masu rauni a gaban mayakan na Jihadi dake ci gaba da haifar masu da mummunar barna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.