Isa ga babban shafi
Najeriya

Cutar nimoniya na iya kashe yara miliyan 2 a Najeriya - UNICEF

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce cutar nimoniya na iya sanadin mutuwar yara kanana har miliyan 2 a Tarayyar Najeriya idan har ba a dau kwararan matakai ba.

Alamar UNICEF
Alamar UNICEF
Talla

A wani sabon nazari da ya firar a ranar Laraba, asusun an UNICEF ya ce kara azama wajen yaki da cutar nimoniya zai ceto yara sama da miliyan 2 daga mutuwa daga cutar da ma sauran cutuka a Najeriya.

Ya ce karancin abinci mai gina jiki, gurbacewar iska, da kuma rashin damar isa ga allurar rigakafi da ma amfani da magunguna masu kashe kwayar cuta ba bisa ka’ida ba sune jigo daga cikin abubuwan dake haddasa mace mace daga cutar nimoniya, wacce a shekarar 2019 ta kashe yaro daya a duk bayan minti 3 a Najeriya.

Wakilin asusun a Najeriya Peter Hawkins ya ce hakkin kawar da barnar da wannan cuta ka iya janyowa ya rataya a wuyar kowa da kowa, saboda haka dole ne a dage don ganin an samu galaba kan wannan cuta ta nimoniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.