Isa ga babban shafi
Libya

Janar Haftar ya baiwa dakarunsa umarnin afkawa sojojin Turkiya

Janar Khalifa Haftar mai iko da yankunan gabashin kasar Libiya, ya baiwa dakarunsa umarnin kaddamar da farmaki kan sojojin dake kasar Turkiya.

Janar Khalifa Haftar mai iko ga gabashin kasar Libya.
Janar Khalifa Haftar mai iko ga gabashin kasar Libya. REUTERS/Esam Omran Al-Fetori/File Photo
Talla

Haftar ya bada umarnin afkawa sojin Turkiya ne sakamakon yadda suka taimakawa sojin gwamnatin hadin giwar Libiya mai samun goyon bayan majalisar dinkin duniya, wajen kwace garuruwa da dama wadanda ke karkashin rundunar mayakansa a baya.

A ‘yan kawanakin da suka gabata, hadin gwiwar sojin gwamnatin Libiya dake Tripoli da na Turkiya suka kwace wani filin jiragen sama dake gaf da birnin na Tripoli, wanda a baya ke hannun mayakan janar Haftar, abinda ke zama babban koma baya ga kwamandan.

Sai dai nasarar gwamnatin ta Libya, ta sanya kasashen dake marawa janar Haftar baya da suka hada da Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Rasha, barazanar kaddamar da farmakin hadin gwiwa kan gwamnatin Libyan mai samun goyon bayan majalisar dinkin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.