Isa ga babban shafi
Malawi

Shugaban Malawi ya bakanta wa 'yan kasar rai kan nadin mukamai

'Yan kasar Malawi sun bayyana bacin ransu kan yadda sabon shugaban kasar Lazarus Chakwera ya bai wa wasu mutane  'yan uwan juna mukaman ministoci bayan nasarar da ya samu a zaben da aka gudanar kwanan nan.

Zababben shugaban Malawi, Lazarus Chakwera
Zababben shugaban Malawi, Lazarus Chakwera AMOS GUMULIRA / AFP
Talla

Daga cikin sunayen ministoci 31 da shugaban ya gabatar, akwai mutane 6 da ke da alaka ta jini a tsakaninsu, duk da cewa ba su hada nasaba da shugaban ba.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya ce, Ministan Kwadago da na Lafiya, 'yan uwan juna ne, yayin da Ministan Yada Labarai ke zama kanwar Mataimakin Ministan Noma.

Tsohon mataimakin Chakwera a zaben shekarar 2019 Sidik Mia ya zama Ministan Sufuri, yayin da matarsa ta zama mataimakiyar Ministar Filaye.

Kungiyoyin Kare Hakkin Bil'adama sun bayyana damuwa kan nade-naden wadanda suka fito daga yankin da shugaban ya fito.

Mkotama Katenga-Kaunda ya ce, daga cikin ministocin 31, kashi 70 sun fito ne daga tsakiyar kasar, kuma guda 9 daga cikinsu daga birnin Lilongwe, inda shugaban ya fito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.