Malawi
Shugaban Malawi ya bayar da kashi 10 na albashinsa don yaki da Covid-19
Shugaban Malawi Peter Muthatirika ya sanar da rage albashinsa da kuma na sauran manyan jami’an gwamnatinsa da akalla 10% domin taimaka wa a yaki cutar Covid-19, tare da daukar wasu karin jami’an kiwon lafiya a cikin gaggawa.
Wallafawa ranar:
Talla
Shugaban ya ce matakin rage albashin ya shafi ministoci da kuma ‘yan majalisar dokokin kasar baki daya har tsawon watanni uku a jere domin taimaka wa al’ummar kasar da wadannan kudade, lura da yadda suke fama da talauci.
Tun ranar 23 a watan jiya ne aka rufe makarantun kasar don hana yaduwar cutar a wannan kasa mai mutane milyan 17.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu