Isa ga babban shafi
Mali

Sojoji sun kama shugaban Mali da Firaministansa

Sojoji masu bore sun kama shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita da Firaministansa Boubou Cisse, inda suka tsare su a sansanin soji da ke garin Kati mai tazarar kilomita 15 daga babban birnin Bamako.Tuni kasashen duniya da suka hada da Amurka da Faransa da Kungiyar Tarayyar Afrika suka fara mayar da martani kan wannan al’amari.

Sojojin Mali da suka yi gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita bore
Sojojin Mali da suka yi gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita bore MALIK KONATE / AFP
Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tattauna batun boren sojin da takwarorinsa na kasashen yammacin Afrika da suka hada da na Nijar da Senegal da Ivory Coast, inda ya nuna goyon bayansa ga yunkurin ECOWAS na shiga tsakani domin samar da masalaha.

Shugaba Macron ya yi tur da boren sojin kamar yadda sanarwar da fadarsa ta Elysee ta fitar ke cewa.

Ita ma Amurka na adawa haramtaccen sauyin da ya saba wa kundin tsarin mulki a Mali kamar yadda jakadanta na musamman a yankin Sahel, J. Peter Pham ya bayyana.

Kungiyar Kasashen Afrika AU ta caccaki kamen da aka yi wa shugabannin biyu na Mali, tana mai bukatar sojojin kasar da su gaggauta sakin su kamar yadda ta bayyana a wani sakon Twitter da shugaban hukumar kungiyar, Moussa Faki Mahamat ya fitar a cikin harshen Faransanci.

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan adawa sun gudanar da jerin zanga-zangar neman shugaba Keita da ya sauka daga karagar mulki bisa zargin gwamnatinsa da cin hanci da rashawa da kuma tabarbarewar tsaro.

Tun da sanyin safiyar Talatar nan, fusatattun sojojin suka fara harbe-herbe a sansaninsu na Kati, yayin da suka karbe iko da hanyoyin da suka ratsa zuwa birnin Bamako.

Boren kifar da gwamnati da aka yi a shekarar 2012 da ya yassare wa shugaba Keita darewa kan karagar mulki, ya taso ne daga wannan sansani na garin Kati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.