Isa ga babban shafi
Afrika

Sabbin mutane miliyan guda sun kamu da kanjamau a Afrika- MDD

Yau ce ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya, inda ake nazari kan matakan da ake dauka na shawo kan wannan cuta da kuma taimakawa dubban mutanen da ke fama da ita a duniya.

Wata mata sabuwar kamuwa da cutar kanjamau a Kampala babban birnin Uganda.
Wata mata sabuwar kamuwa da cutar kanjamau a Kampala babban birnin Uganda. REUTERS/Euan Denholm
Talla

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce yanzu haka mutane miliyan 38 ke dauke da cutar a duniya, kuma kasha 67 daga cikin su suna nahiyar Afirka ne.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce a shekarar 2019 mutane sama da miliyan guda suka harbu da cutar a nahiyar Afirka, adadin da ya kai kashi 60 na sabbin masu dauke da cutar a fadin duniya, yayinda wasu dubu 440 suka mutu sakamakon cutar.

Taken bikin na bana dai shi ne hadin kai da daukar nauyi saboda muhimmancin shawo kan cutar kamar yadda ake samu a yau dangane da cutar korona, wadda ta sanya gwamnatoci da al’ummomi daukar matakai da kuma inganta yadda ake kare yada cutar da kula da masu fama da ita.

Babbar jami’ar Hukumar Lafiya ta Duniya dake kula da shiyar Afirka Dr Matshidiso Moeti ta ce annobar korona na yiwa aikin kula da masu dauke da cutar korona illa, abinda ya sa ba’a iya gano yaran dake dauke da cutar domin kula da su, ganin yadda mata da yara dake tsakanin shekarar 15 zuwa 24 ke kashi 37 na sabbin masu dauke da cutar ta HIV a duniya.

Jami’ar tace duk da matsalolin da ake fuskanta, an samu cigaba a shekara ta 2020, ganin yadda kasha 81 na masu dauke da cutar sun san matsayin su, yayin da kashi 70 daga cikin sun a manya da kashi 53 na yara ke samun taimakon maganin rage radadin cutar, cikin su harda kashi 85 na mata masu ciki da masu shayarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.