Isa ga babban shafi
Afrika

Mutane 41 ne suka mutu a hadarin kwale-kwale a Uganda

Akala mutane 41 ne suka rasa rayukan su a wani hadarin jirgin kwale-kwale dauke da fasinjoji saman kogin Albert dake kan iyakokin kasashen Uganda da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo .

Masunta a saman kogi Albert
Masunta a saman kogi Albert Creative Commons CC BY-NC 2.0 Flickr/ Jurriaan Persyn
Talla

Hadarin ya auku ne tun ranar laraba,masu bincike sun gano cewa jirgin na dauke da kusan mutane 50 ne kafin aukuwar hadarin.

Masu aikin ceto sun samu nasarar tsamo gawarwakin mutane 41,tareda ceto wasu daga cikin fasinjojin a cewar daya daga cikin jami’an dake aiki da hukumomin Uganda Ashraft Oromo.

Ana ci gaba da neman sauren mutane dake cikin wannan jirgi, yayinda hukumomin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo suka tabbatar da mutuwar mutane 41,an ceto 7 da ran su.Rahotanni dai sun ce iska mai karfin gaske ne ya kifar da jirgin a tsakaddaren ranar Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.