Isa ga babban shafi
Uganda

An yi min barazanar kisa a Uganda- Bobi Wine

Magudun ‘yan adawan Uganda Bobi Wine ya ci gaba da nuna turjiya bayan sakin sa daga gidan yari jim kadan da arangamar da magoya bayansa suka yi da jami’an tsaro, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 37.

Bobi Wine da tawagarsa
Bobi Wine da tawagarsa SUMY SADURNI / AFP
Talla

An gudanar da zanga-zangar kwanaki biyu don nuna adawa da cafke Wine gabanin gangamin yakin neman zabensa, yayin da ake sa ran zai fafata da shugaba Yoweri Museveni a zaben watan Janairu mai zuwa.

A wannan Juma’ar aka tuhumi Wine kan keta ka’idojin takaita bazuwar cutar coronavirus tsakanin jama’arsa da ke halartar manyan tarukan siyasa. Kodayake kotu ta bada belinsa.

A yayin zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP, Wine wanda mawaki ne da ya shiga fagen siyasa ya ce, an azabtar da shi tare da yi masa barazanar kisa a gidan yarin da aka garkame shi.

Sai dai madugun ‘yan adawan ya bayyana cewa, babu abin da zai hana shi ci gaba da fafutukarsa ta nema wa al'ummar Uganda makoma ta gari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.