Isa ga babban shafi
Uganda

Uganda ta nemi Google ya rufe wasu tashoshin Youtube 14 na 'yan kasar

Gwamnatin Kasar Uganda ta bukaci kamfanin Google da ya mallaki YouTube da ya rufe wasu tashoshi 14 da ake amfani da su wajen yada labaran zanga zangar da akayi a watan jiya wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 50.  

Shugaban kasar Uganda Yuweri Museveni.
Shugaban kasar Uganda Yuweri Museveni. Ug.gov
Talla

Hukumar kula da sadarwar kasar ta rubuta wasika ga kamfanin inda ta ke bayyana damuwa kan yadda aka yı amfani da tashoshin YouTube wajen tinzira jama’a su yi zanga zangar.

An gudanar da zanga zangar ne a birnin Kampala da wasu biranen kasar bayan kama Robert Kyagulanyi ko kuma Bobi Wine da aka zarga da karya ka’idar kaucewa kamuwa da cutar korona da aka saka.

Ana dai ci gaba da samun takun-saka tsakanin Bobi Wine dan takarar shugabancin kasar da kuma gwamnatin Uganda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.