Isa ga babban shafi

François Hollande da wasu mutane daban sun bukaci a sako Marafa Hamidou Yaya

Tsohon sakatare janar na fadar shugaban kasar Kamaru Marafa Hamidou Yaya, wanda aka tsare da shi tun shekarar 2012 , dan siyasar mai shekaru 71, ya shigar da kira  na neman ganin an sako shi sabili da yanayin lafiyarsa bayan ci gaba da tsare shi gidan kurkuku.

Tsohon ministan cikin gida na Kamaru Marafa Hamidou Yaya, a zaman kotu a  Yaoundéranar 16 ga watan yuli na shekarar 2012.
Tsohon ministan cikin gida na Kamaru Marafa Hamidou Yaya, a zaman kotu a Yaoundéranar 16 ga watan yuli na shekarar 2012. © REINNIER KAZE/AFP
Talla

 Tsohon sakatare janar na fadar shugaban kasar ta Kamaru da aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari saboda samun sa da laifin almubazzaranci da kudin jama'a", ya shigar da wannan koke ne bayan da mujalar Jeune Afrique da ta samu hira da shi, ta kuma falasa halin da yake ciki a yanzu haka.

Kiran tsohon na hannun damar shugabar kasar ta Kamaru Marafa Hamidou Yaya ya shiga kunen wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar kasashen Duniya,inda tuni dai tsohon shugaban Faransa François Hollande da wasu mutanen daban suka yi kira da a sake shi saboda rashin lafiya.

Tsohon Sakataren fadar shugaban kasar Kamaru  Marafa Hamidou Yaya.
Tsohon Sakataren fadar shugaban kasar Kamaru Marafa Hamidou Yaya. AFP PHOTO DESIREY MINKOH

Marafa Hamidou Yaya na fama da rashin gani ko cutar glaucoma, rahotani na bayyana cewa ya rasa amfani da idonsa na dama.

 Marafa Hamidou Yaya ya na mai bayyana damuwa da gudu kada ya rasa idonsa daya cilo da ya rage,yayin wannan hira da mujalar ta Jeune Afrique ya ke mai bayyana cewa likitoci sun bayar da shawarar a yi masa tiyata wanda hakan zai ceto shi daga zama makaho.

Tsohon Sakataren fadar shugaban kasar Kamaru kuma tsohon Ministan cikin gida Marafa Hamidou Yaya
Tsohon Sakataren fadar shugaban kasar Kamaru kuma tsohon Ministan cikin gida Marafa Hamidou Yaya © REINNIER KAZE/AFP

 Marafa Hamidou Yaya  wanda ya ci gaba da bayyana damuwa ganin halin ko in kula daga Shugaban kasar ta Kamaru Paul Biya a wannan bukata ta shi, ya na mai shigar da wannan koke da cewa ya zuwa wannan lokaci,ba shi da masaniya bisa dalilan ci gaba da tsare shi da ake yanzu haka a gidan yari,a karshe ya na mai cewa wasu daga cikin mutane da aka kama shi da su a lokaci, an sake su a halin yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.