Isa ga babban shafi
Afrika

Gwamnatin Mali ta tabbatar da ikirarin Faransa na kashe yan ta'adda

Gwamnatin Mali ta tabbatar ikirarin rundunar sojin Faransa na halaka gwamman mayaka masu ikirarin jihadi a yankin Douentza-Hombori dake tsakiya kasar ta Mali a ranar lahadin da ta gabata; farmakin da wasu mazauna yankin suka ce ya halaka fararen hula akalla 18, dake halartar bikin aure ne a maimakon ‘yan ta’adda.

Dakarun Faransa a Menaka na kasar Mali
Dakarun Faransa a Menaka na kasar Mali Reuters
Talla

Rundunar sojin Faransa ta musanta yin kuskure a farmakin, inda ta jaddada cewar ‘yan ta’adda akalla 30 ta halaka, kuma bata kaddamar da harin ba sai bayan gudanar da cikakken bincike, ikirarin da gwamnatin Mali ta marawa baya.

Da jimawa kungiyoyi  na zargin Faransa da kai hari saman farraren hula a yankin Sahel, wanda kuma bincike ke iya tabbatarwa,to sai dai Faransa a koda yaushe ta kaddamar da irin wannan farmaki,ta kan kawo sheida dake tabbatar da cewa yan ta'adda ne ta halaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.