Isa ga babban shafi
Algeria

Algeria za ta yiwa kundin tsarin mulkinta garambawul tare da kiran zaben gaggawa

Shugaba Abdelmadjid Tebboune na Algeria ya sanar da yafiya ga daukacin mutanen da ake tsare da su a gidajen yari saboda samunsu da laifin caccakar gwamnati, inda a bangare guda kuma ya sanar da shirin kiran zabe cikin gaggawa dai dai lokacin da ya ke cika shekara 2 a karagar mulki.

Shugaban kasar ALgeria Abdelmadjid Tebboune.
Shugaban kasar ALgeria Abdelmadjid Tebboune. REUTERS/Ramzi Boudina
Talla

Algeria wadda ke gaba da fuskantar manyan kalubale kama daga tattalin arziki da rikicin siyasa baya ga annobar Coronavirus da ta sake haddasa matsin rayuwa har yanzu matasa na ci gaba da boren ganin an samar da gagarumin sauyi a mulkin kasar.

Kalaman Tebboune da ya gabatar ga daukacin al’ummar kasar yayin bikin cika shekaru 2 a mulkin na zuwa dai dai lokacin da sabuwar zanga-zanga ke sake barkewa a sassan kasar, shugaban ya yi umarnin rushe majalisar kasar yayinda ya yi alkwarin garambawul ga kundin tsarin mulki.

A kalaman Tebbourne jiya Alhamis ya ce yana fatan samar da kakkarfar majalisar kasar da za ta kunshi matasa zalla.

Shugaban na Algeria ya sha alwashin aiwatar da garambawul din cikin kasa da sa’o'i 48 masu zuwa garambawul din da acewarsa zai samar da dokar da za ta bayar da damar gudanar da sahihin zabe tare da zuba matasa a mukamai kamar yadda al’ummar kasar ke bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.