Spain ta tasa keyar 'yan ci rani fiye da dubu 6 zuwa Morocco
Ma’aikatar harkokin cikin gidan Spain ta sanar da maida ‘yan ci rani fiye da dubu 6 da 500 da suka ketara cikin kasar zuwa Morocco.
Wallafawa ranar:
Sanarwar tace adadin ‘yan ci ranin da aka maida Moroccco na daga cikin jumillar dubu 8 ne da suka ketara zuwa tsibirin Cueta dake kasar ta Spain a farkon makon nan mai karewa.
Bayanai sun ce hukumomin Morocco sun sun sassauta matakan tsaron dake kan iyakarsu da yankin Cueta na Spain a baya bayan nan, matakin da wasu masharhanta ke kallo a matsayin raddi ga gwamnatin Spain saboda karbar bakuncin jagoran masu fafutukar kafa kasar Plisario Brahim Ghali, wanda tun a watan jiya yaje kasar ta Spain domin duba lafiyarsa.
Sai dai yayin ganawa da manema labarai a jiya, ministan cikin gidan Spain Fernando Grande-Marlaska, ya bayyana fatan kawo karshen tsamin dangantakar da ta kunno kai tsakanin su da Morocco nan bada dadewa ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu