Algeria ta soke lasisin France 24
Algeria ta soke lasisin da ke bai wa wakilan tashar talabijin ta France 24 damar gudanar da ayyukanta a cikin kasar.
Wallafawa ranar:
Sanarwa da ma’aikatar watsa labaran Algeria ta fitar a marecen jiya lahadi, ta ce an dauki matakin ne lura da yadda ta nuna son-kai wajen yada zanga-zangar masu hamayya da gwamnatin kasar.
Sai dai France Media Monde, da ke matsayin shugabar rukunin kafafen yada labaran Faransa masu watsa shirye shirye zuwa kasashen ketare ta bayyana mamaki kan matakin da gwamnatin Algerian ta dauka.
A baya bayan nan kungiyar ‘yan jaridu ta duniya RSF ta sanya Algeria a matsayi na 146 daga cikin kasashe 180 da suke mutunta aikin jarida da fadin ‘yancin albarkacin baki.
Gwamnatin Algeria dai ta shafe kusan shekaru 2 tana fama da zanga-zangar neman sauyi karkashin kungiyar Hirak da dubban ‘yan kasar suka kafa domin kawar da gwamnatin tsohon shugaban kasar AbdulAziz Bouteflika, bayan da yayi yunkurin zarcewa bisa shugabancin kasar karo na 5 a jere cikin shekarar 2019.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu