Isa ga babban shafi
Kamaru - Biya

Kotu a Geneva da daure masu zanga zangar adawa da Paul Biya

Kotu a kasar Switzerland ta yanke hukuncin dauri kan ‘yan asalin kasar Kamaru su 12 da ke zaune a kasar saboda gudanar da zanga-zanga a harabar wani otel da aka shugaba Paul Biya da da matarsa suka sauka a birnin Geneva.

Wasu 'yan kasar Kamaru mazauna Turai dake zanga zangar adawa da gwamnatin Paul Biya a Brussel, 17 ga watan Yuli 2020.
Wasu 'yan kasar Kamaru mazauna Turai dake zanga zangar adawa da gwamnatin Paul Biya a Brussel, 17 ga watan Yuli 2020. AP - Francisco Seco
Talla

Magoya bayan kungiyar da ake kira Brigade Anti-Sardinards wadda ta kunshi ‘yan adawar Kamaru da ke zaune a kasashen Tura ne suka gudanar da wannan zanga-zanga a ranar 17 ga wannan wata Yuni duk da cewa mahukuntan kasar ta Switzerland sun haramta gangamin.

A lokacin zanga-zangar an kama kusan mutane 100 bisa zargin yunkurin mamaye otel din da shugaba Paul Biya da uwargidansa Chantal suka sauka, kuma daga cikin wadanda aka kama har da Calibri Calibro da aka bayyana cewa shi ne jagoran masu tarzomar.

Daga bisani dai ‘yan sanda suka saki mafi yawan mutanen, yayin da aka gurfanar da sauran gaban kotu wadda ta yanke hukunci kan 12 daga cikinsu, hukuncin da ya kama daga daurin talala da kuma tara, yayin da wasu za su share tsawon kwanaki 40 zuwa 180 a gidan yari.

Majiyoyi sun ce tuni lauyan da ke kare mutanen ya ce zai daukaka kara dangane da hukuncin da aka yanke masu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.