Isa ga babban shafi
Kamaru - 'Yan aware

'Yan bindiga sun kashe mutum 1 tare da jikkata limamin Coci a Bali

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wata mujami’a da ke Kamaru inda suka kashe mutum guda, suka kuma raunata limamin cocin a yankin da ake amfani da turancin Ingilishi.

Wasu jami'an tsaron kasar Kamaru a garin Buea.
Wasu jami'an tsaron kasar Kamaru a garin Buea. © Marco Longari/AFP
Talla

Shugaban reshen cocin Samuel Fonki ya ce ‘yan bindigar sun bude wuta kai mai uwa da wabi ne a mujami’ar da ke garin Bali a daidai lokacin da ake gudanar da ibada.

Fonki ya ce limamin cocin ya samu harbin bindiga a hannun sa a harin da ake zargin mayakan ‘yan aware ne suka kai.

Jami'ai sun ce ‘yan bindigar sun yi kokarin kai farmaki ne kan wasu sojoji da ke kusa amma harin ya fada kan masu ibadar da ke mujami’a.

Bincike dai ya gano cewar maharan sun fara ajiye  nakiyoyi a gefen hanya ne, amma sojojin suka yi nasarar kaucewa don haka suka bude wuta.

Yadda rikicin 'yan awaren Kamaru ya samo asali

Tsirarun masu magana da turancin Ingilishi a lardunan yammacin Kamaru sun dade suna korafin cewa masu rinjaye da ke Magana da harshen Faransanci da shugaba Paul Biya mai shekaru 88, da ke mulki na tsawon shekaru 38 sun mayar da su saniyar ware.

Zanga -zangar da suka yi ta rikide zuwa kazamin rikicin ya baiwa ‘yan awaren damar samar da mayakan da a yanzu ke kai hare-hare kan ‘yan sanda, sojoji da kuma fararen hula.

Fiye da mutane dubu 3 da 500 aka kashe yayin da wasu sama da dubu 700 suka tsere daga gidajensu don gujewa rikicin da ya barke a shekarar 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.