Isa ga babban shafi
Rwanda-Afghanistan

Rwanda za ta karbi dalibai mata daga Afghanistan

Rwanda za ta karbi dalibai mata 250 da suka baro Afghanistan biyo bayan karbe ragamar mulkin kasar da mayakan Taliban suka yi don su karashe karatunsu  a kasar da ke gabashin nahiyar Afirka.

Shugaban Rwanda, Paul Kagame.
Shugaban Rwanda, Paul Kagame. © RFI
Talla

Shabana Basij-Rasikh, shugabar wata makarantar koyar da shugabanci ta Afghanistan ta ce wadannan dalibai mata da malamansu na kan hanyarsu ta zuwa Rwanda daga Qatar, don fara wani zangon karatu a kasar waje.

Basij-Rasikh ta ce suna fatan zama na wucin gadi a Rwanda har zuwa lokacin da al’amura za su daidaita a Afghanistan, inda ta kara da cewa tana cikin tashin hankali a game da abin da ke faruwa a kasarta.

Dimbim al’ummar Afghanistan sun kagara su bar kasar tasu bisa tsoron kasancewa a karkashin mulkin kungiyar Taliban, kuma dubbai ne daga cikinsu aka kwashe zuwa wasu kasashe.

Kungiyar Taliban, wadda ta yi mulki bisa tsatsaurar tsarin mulkin Islama a kasar daga shekarar 1995 zuwa 2001, ta sake karbe iko da Afghanistan fiye da mako daya da ya gabata.

A wani sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter, ma’aikatar ilimi na Rwanda ta yi maraba da wadannan dalibai mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.