Isa ga babban shafi
Kamaru - 'Yan aware

Harin 'Yan aware ya hallaka sojojin BIR da dama a Kamaru

Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa sojojin rundunar yaki da ta’addanci wato BIR da dama suka hallaka a tsaunin Sabga dake yankin Arewa maso yammacin kasar da ake amfani da Turancin Ingilishi, sakamakon wani harin kwantar bauna da mayakan ‘yan aware suka kaddamar.

Dakarun BIR dake fafatawa da 'yan aware a yankunan Arewa maso yammaci da Kudancin Kamaru.
Dakarun BIR dake fafatawa da 'yan aware a yankunan Arewa maso yammaci da Kudancin Kamaru. © AFP - STRINGER
Talla

Wasu faye-fayen bidiyo da jaridun kasar ta Kamaru suka wallafa, sun nuna gomman gawarwakin sojojin kwance da kuma motarsu ta silke na ci da wuta, yayin da ake kallon maharan na ‘yan aware dauke da makamai suna Magana cikin Turancin PIDGIN.

Wannan na zuwa ne kasa da mako guda bayan da sojojin kasar akalla tara suka gamu da ajalinsu sakamakon hare-hare maban-banta da mayakan ‘yan aware dake neman ballewa don kafa jamhuriyar Ambazonia suka kaddamar a yankin arewa maso yammaci da ake amfani da turancin Ingilishi.

Ya zuwa yanzu rundar sojin Kamaru ko gwamnati basu ce uffan ba, dangane da hare-haren na yankin renon Ingila da ya dauki kusan shekaru hudu ana fafatawa da ‘yan aware masu dauke da makamai dake neman ballewa domin kafa kasar Ambazonia, wanda ya yi sanadiyar salwantar rayukan sama da mutane 3500 ciki harda jami’an tsaro dubu daya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.