Isa ga babban shafi
Algeria

Jana'izar Bouteflika ba ta samu karramawar musamman ba

An gudanar da jana’izar tsohon shugaban kasar algeriya Abdelaziz Bouteflika ba tare da girmamawar da ake yiwa tsoffin shugabannin kasar ba.

Tsohon shugaban kasar Algeria Abdelaziz Bouteflika, 27/03/2009
Tsohon shugaban kasar Algeria Abdelaziz Bouteflika, 27/03/2009 © AP - Alfred de Montesquieu
Talla

Tsohon shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika, wanda shi yafi kowanne shugaban Algeria dadewa a karagar mulki, ya rasu ne ranar juma’a yana da shekaru 84 a duniya.

An gudanar da jana’izar ba tare da karrama gawar sa ba kamar yadda aka saba, da kuma zaman makoki na kwanaki 3 maimakon 8 da ake yiwa tsoffin shugabanni, abinda ke nuna yadda jama’ar kasar ke kallon sa.

Bouteflika ya fara zama ministan harkokin waje ne a shekarar 1960, kafin daga bisani ya zama shugaban kasa a shekarar 1999.

Daga cikin wadanda suka halarci jana’izar sa harda shugaban kasa Abdelmajid Tebboune da ministan ‚yancin kasa Laid Rebiga wanda ya karanta tarihin sa, sai kuma jami’an gwamnati da na diflomasiya, a bikin da akayi cikin matakan tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.