Isa ga babban shafi
Malawi

Tsohon Kakakin Majalisa ya bindige kansa don kin amsa tambaya

Wani tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin Malawi ya bindige kansa har lahira a farfajiyar majalisar a yayin halartar wani zaman sauraren bahasi kan wata tuhuma da ake masa.

Clement Chiwaya, tsohon mataimakin Kakakin Majalisar Malawi da ya harbe kansa har lahira
Clement Chiwaya, tsohon mataimakin Kakakin Majalisar Malawi da ya harbe kansa har lahira © Dateline Nigeria
Talla

Clement Chiwaya, mai shekaru 50 ya dankara wa kansa harsashi ne a cikin zauren majalisar, inda ya halarci zaman wani kwamiti da ya bukaci ya yi bayani a game da motar da aka ba shi a shekarar 2019, a lokacin da yake kan mukaminsa na kakaki.

Kakakin ‘yan sandan kasar, James Kadadzera ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma kuma bai bada karin bayani ba, bisa dalilin cewa sai ya karbi cikakken rahoto daga masu bincike.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.