Isa ga babban shafi
Mali - Ta'addanci

An kashe dakarun Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali

Majalisar Dinkin Duniya ta ce wani sojan wanzar da zaman lafiyar ta dan kasar Masar ya mutu sannan abokan aikinsa hudu sun samu munanan raunuka sakamakon hari da bama-bamai da aka kai kan jerin gwanon motocinsu a arewacin kasar Mali mai fama da tashin hankali ranar Asabar.

Jami'an wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali 13 ga watan Mayu 2015.
Jami'an wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali 13 ga watan Mayu 2015. REUTERS/Adama Diarra
Talla

Da yake tabbatar da adadin, mai magana da yawun babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya ce Antonio Guterres ya yi kakkausar suka dangane da hare-haren wadanda suka auku a kusa da Tessalit, kusa da kan iyakar Malai da Aljeriya.

Guterres ya ce hare -haren na iya zama laifukan yaki, don haka ya yi kira ga hukumomin Mali da su “ba da himma” wajen gano wadanda ke da alhakin hakan.

Kasar Mali dake fama da hare-hare daka masu ikirarin jihadi, ta fada cikin rudanin siyasa tun bayan juyin mulkin da sojoji sukayi a watan Agustan shekarar 2020, inda aka kafa gwamnatin farar hula ta wucin gadi, wanda itama aka sake hambarar da ita a karo na biyu kasa da shekara guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.