Isa ga babban shafi
HUKUNCIN-KISA

Saliyo ta kawo karshen aiwatar da hukuncin kisa

Shugaban Saliyo Julius Maada Bio ya sanya hannu akan dokar soke aiwatar da hukuncin kisa, inda ya bayyana cewar kasar sa ta kawo karshen hukuncin saboda rashin imanin dake tattare da shi.

Shugaban Saliyo Julius Maada Bio
Shugaban Saliyo Julius Maada Bio © AFP - Kola Sulaimon
Talla

Bio ya sanya hannu akan dokar ce lokacin wani biki da aka gudanar a Freetown bayan majalisar dokoki ta amince da dokar a watan Yulin wannan shekara.

Shugaban wanda ya danganta aiwatar da hukuncin kisan a matsayin rashin imani, yace ayau sun tabbatar da matsayin su na mutunta ran Bil Adama.

Kasar Saliyo wadda ke ci gaba da farfadowa daga yakin basasa, ta sha samun suka daga kungiyoyin kare hakkin ‘Dan Adam saboda amfani da dokar hukuncin kisa.

Mataimakin ministan shari’ar kasar Umaru Napoleon Koroma yace kasar ta su ta fara aiwatar da hukuncin kisa ne tun daga shekarar 1798, kusan shekaru 10 bayan Turawan mulkin Birtaniya sun samar da yankin dake dauke da bayin da suka samu ‘yanci a shekarar 1787.

A shekarar da ta gabata ta 2020 akalla mutane 94 ke jiran aiwatar musu da hukuncin kisan, wanda tun daga shekarar 1998 aka daina aiwatar da shi, sai dai daurin rai-da-rai.

Kundin tsarin mulkin Saliyo na shekarar 1991 ya bada damar aiwatar da hukuncin kisa akan wadanda aka tabbatar da lafin fashi da makami akan su ko kisan kai ko cin amanar kasa ko kuma yiwa kasa bore.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.