Masu adawa da juyin mulki a Sudan sun shirya gagarumar zanga-zanga
Masu adawa da juyin mulkin Sudan na shirin gudanar da gagarumin zanga-zanga ranar Asabar domin Allah wadai da matakin sojoji na kawar da fararen hula wanda ya kawo cikas ga gwamntin rikon kwarya tare da haifar da kazamin rikici.
Wallafawa ranar:
Matakin sojin Sudan dai ya janyo ce-ce-ku-ce daga kasashen duniya, inda Amurka da Majalisar Dinkin Duniya suka bukaci shugabannin sojojin da su yi taka tsantsan.
Janar Abdel Fattah al-Burhan – wanda ke jagorantar bangare soji a gwamnatin rikon kwaryar hadakar su da farar hula a Sudan tun bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir a shekarar 2019 bayan zanga-zangar da matasa suka jagoranta - ya jagoranci kwace mulki a ranar Litinin.
Ya rusa gwamnatin kasar da farar hula ke jagoranta, ya kuma ba da umarnin tsare wasu manyan jami'an farar hula tare da kafa dokar ta baci a fadin kasar.
Akalla masu zanga-zangar 8 ne suka mutu sannan wasu 170 suka jikkata sakamakon arangamar da suka yi da jami’an tsaro, wadanda suka harba barkonon tsohuwa, da harbi da harsasan roba, a cewar likitoci. An kama wasu masu fafutukar tabbatar da dimokradiyya.
Sai dai a jajibirin taron na ranar Asabar, wani jami’in Amurka ya ce adadin wadanda suka mutu ya kai tsakanin 20 zuwa 30, ya kuma kara da cewa zanga-zangar za ta kasance “kalubale” ga aniyar sojojin Sudan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu