Isa ga babban shafi
HADARIN-SALIYO

Mutane 92 suka mutu a gobarar Saliyo - Mataimakin Shugaban kasa

Gwamnatin Saliyo tace adadin da mutanen da suka mutu sakamakon gobarar da ta tashi a wani gidan mai ya kai 92, abinda yayi sanadiyar konewar motoci da mutanen dake ciki.

Yadda wuta ta kona mutane da ababan hawa a gidan man Saliyo
Yadda wuta ta kona mutane da ababan hawa a gidan man Saliyo via REUTERS - NATIONAL DISASTER MANAGEMENT AGE
Talla

Hukumomin kula da lafiya a kasar ta ce gawarwakin da suka tantance sakamakon hadarin da ya faru daren jiya ya kai 92, yayin da ake danganta hadarin da kama wutar da wata mota tayi.

Cikin wadanda hadarin ya ritsa da su akwai mata da maza da kuma yara, a hadarin da ya janyo daruruwan mutane da masu aikin agaji zuwa wurin tun daren jiya.

Masu aikin agaji a gobarar gidan man Saliyo
Masu aikin agaji a gobarar gidan man Saliyo AFP - SAIDU BAH

Shugaban kasa Julius Maada Biyo ya bayyana kaduwar sa da hadarin wanda ya kaiga asarar tarin rayuka, yayin da ya aike da sakon ta’aziya ga ‘yan uwa da iyalan wadanda hadarin ya ritsa da su.

Shugaba Biyo yace gwamnatin sa zata yi abinda ya dace wajen taimakawa iyalan wadanda hadarin ya ritsa da su.

Mai rike da mukamin Magajin Garin Freetown Yvonne Aki-Sawyerr ta bayyana bacin ran ta da hadarin, wanda tace yana tada hankalin duk wadanda suka ga bidiyon da aka yada ta kafofin sada zumunta.

Aki-Sawyerr tace rahotanni da suke samu sun ce adadin mutanen da suka mutu na iya zarce 100, amma babu wani tabbaci daga hukumomi akai.

Mataimakin shugaban kasa Mohammed Juldeh Jalloh ya ziyarci wurin hadarin yau da safe inda ya tabbatar da mutuwar mutane 92, yayin da yace wasu 88 ke asibiti ana kula da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.