Babu inda 'Yan ta'adda suka mallaki manyan makamai kamar Sahel - Bazoum
Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya bayyana cewar ba karamar kuskure akayi ba wajen gaza dakile safarar makaman dake fitowa daga kasar Libya wadanda ‘Yan ta’adda ke amfani da su wajen kai munanan hare hare a Yankin Sahel.
Wallafawa ranar:
Bazoum yace kasashen Sahel na bukatar taimako daga kawayen su na duniya wajen tattara bayanan asiri da jiragen yaki da kuma horar da jami’an tsaro domin tinkarar matsalar tsaron da ta addabi yankin.
Dangane da batun tattara bayanan asiri, shugaban Nijar yace babban kuskuren abokan aikin su shine rashin sanya hannu wajen yaki da safarar makaman dake fitowa daga Libya, abinda ya bayyana shi a matsayin babban ginshikin rura wutar hare haren ta’addanci.
Yanzu haka sojojin kasashen Sahel da wasu kasashen Turai cikin su harda Faransa na fafatawa da ‘Yan ta’adda a Yankin wajen dakile hare haren da suke kaiwa.Shugaban yace kungiyoyin ‘Yan ta’addan dake kai hare hare a Yankin Sahel sun banbanta sakamakon kazaman makaman da suke dauke da shi, wadanda suke samu cikin sauki daga masu safarar su daga kasar Libya.
Bazoum yace wani lokaci ya kan yi tunanin cewar wasu makaman da ‘Yan ta’addan ke dauke da shi ya zarce na sojoji, musamman ganin irin samfurin makaman harba makamin roka da ake kira RPG da kuma bindigogi masu sarrafa kan su da ake kira M80 da suka mallaka.
Shugaban yace babu wani yanki na duniya da ‘Yan ta’adda suka mallaki irin wadannan kazaman makamai kamar yadda suke da shi a yankin Sahel.Tun daga shekarar 2011 lokacin da aka kashe shugaban Libya Muammar Ghadafi kasar ta fada cikin rudani da tashin hankali da kuma rikicin kabilancin wanda wani lokaci kasashen ketare ke rura wutar sa.
Bazoum yace tumbatsar makaman kasar zuwa yankin Sahel ya taimakawa ‘Yan ta’adda tare da wasu kungiyoyin ‘Yan bindiga wadanda ke aikata manyan laifuffuka kamar yadda ake gani yau a Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu