Isa ga babban shafi

'Yan Sandan Faransa na tsare da 'yan Algeria sama da 50

‘Yan sanda a kasar Faransa sun ce akalla mutane sama da 50 aka kama a karshen mako lokacin da magoya bayan kasar Algeria suka gudanar da murnar nasarar da kasar ta samu wajen lashe kofin kwallon kafar kasashen Larabawa, kuma akasarin su an kama su ne kusa da fadar shugaban kasa.

Tawagar kungiyar kwallon kafar Algeria
Tawagar kungiyar kwallon kafar Algeria Reuters
Talla

Sanarwar Yan Sandan tace a birnin Paris kawai mutane 32 aka tsare, yayin da aka gargadi 432, akasarin su saboda karya dokar tuki a tsakiyar birnin.

Kungiyar kwallon kafar Algeria ta lashe kofin kasashen Larabawa
Kungiyar kwallon kafar Algeria ta lashe kofin kasashen Larabawa DENOUR AFP

Algeriya ta doke Tunisia da ci 2-0 a wasan karshe da aka kara a Qatar wajen lashe kofin, abinda ya sa magoya bayan kasar a biranen Faransa da suka hada da Paris da Lyon da kuma Roubaix suka fantsama tituna domin nuna murnar su.

Kasa da makonni uku kenan da Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya isa Algeria a wani yunkuri na gyara alakar kasashen biyu bayan sabanin da suka samu a baya-bayan nan wanda ya kai ga musayar janye jakadun juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.