Shugaban Botswana ya kamu da cutar Covid 19
Gwamnatin Botswana ta sanar da cewa shugaban kasar Mok-gweetsi Masisi ya harbu da cutar Covid 19. kasar Botswana da Africa ta Kudu sun kasance kasashe biyu da aka fara gano sabon nau'in cutar Korona na Omicron.
Wallafawa ranar:
Yayinda wasu kasashen Afrika ke iya kokarin ganinj jama'ar su sun karbi allurar rigakafin cutar Covid 19,bulluwar sabon nau'in cutar Omicron ya dada saka jama'a cikin shaku.
A Afrika ta Kudu da wasu kasashen daban ,hukumomi tareda hadin gwiwar jami'an kiwon lafiya na iya kokarin ganin an takaita adadin masu kamuwa da wannan cuta.
A Botswana yan lokuta da sanar da cewa shugaban kasar ya kamu da kwayar cutar ,jami'an gwamnatin sun ce shugaban kasar ta su baya cikin mummunar yanayi, kuma jikinsa bai nuna yana dauke da wannan cuta, amman mataimakinsa ne zai ci gaba da gudanar da harakokin gwamnati .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu