Isa ga babban shafi
Corona-Congo

Tsoron karbar rigakafin corona ya tilasta 'yan Rwanda tserewa Congo

Mahukuntan Rwanda sun sanar da tserewar daruruwan ‘yan kasar zuwa makwabciyarta Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo cikin kwanakin baya-bayan nan a wani yunkuri na gujewa karbar allurar rigakafin covid-19.

Wani da ke karbar rigakafin corona a Rwanda. 
Wani da ke karbar rigakafin corona a Rwanda.  Ludovic MARIN AFP/File
Talla

Acewar Ofishin kula da yawan jama’a na tsibirin Idjwi da ke gab da lardin Kivu a ‘yan kwanakin akwai ana samun turuwar mutanen da ke tsallakowa kasar daga  Rwanda ta hanyar amfani da iyakar ruwan da ke tsakanin kasashen biyu.

Shugaban Ofishin Karongo Kalaja ya ce kananun tawagogi dauke da tsirarun mutane da zuwa yanzu suka haura mutum 100 na shiga kasar ta hanyar amfani da kananun jiragen kwale-kwale.

Acewar Ofishin yanzu haka suna tattaunawa da mutanen kuma galibi dalilansu baya wuce gujewa karbar rigakafin na corona da mahukuntan Rwanda ke tsaurara matakai akansu.

Idee Bakalu, shugaban al’ummar yankin Bukavu gari mafi girma a lardin kudancin Kivu ya ce zuwa jiya talata sun karbi mutanen da yawansu ya kai 101 a iya garin Ntambuka.

Sai dai shugaban kungiyar fararen hular Idjwi Esther Muratwa ya ce adadin ‘yan Rwanda da suka samu masauki a hannunsu sun kai 123 dukkaninsu suna ikirarin gujewa rigakafin corona.

 Rwanda mai yawan jama’a miliyan 13 ta sanya tsauraran matakan tilasta karbar allurar rigakafin corona don dakile cutar, inda zuwa yanzu ta yiwa mutane miliyan 4 da dubu 200 rigakafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.