Isa ga babban shafi
Mali-Jamus

Jamus ta fusata da matakin Mali na hana jirginta sauka a kasar

Jamus ta fusata da matakin mahukuntan Mali na kin sahalewa wani jirginta kirar Airbus A400M dauke da sojoji 80 sauka a kasar wanda ya tilasta masa karkata akalarsa zuwa birnin Yamai na Jamhuriyyar Nijar.

Jirgin Sojin Jamus da ya karkata akalarsa zuwa Yamai bayan hanshi sauka a Mali.
Jirgin Sojin Jamus da ya karkata akalarsa zuwa Yamai bayan hanshi sauka a Mali. © RFI/Franck Alexandre
Talla

Rundunar sojin ta Jamus a wani sakonta ta shafin Twitter ta ce, yanzu haka dai an karkata jirgin zuwa babban tsibirin Canarie", na kasar Spain kafin tabbatar da haske dangane lamarin".

Bada jimawa ba dai ne, mahukumtan mulkin sojin kasar Mali suka taikata zirga zirgar jiragen sama sojin kasashen duniya da ke cikin rundunar tsaron Majalisar Dinkin Duniya MIMUSMA da ke Mali, da sojojin kasar ta Jamus ke ciki.

Wani kakakin ma’aikatar harakokin wajen Jamus a ranar litanin ya tabbatar da cewa tun ranar alhamis da ta gabata ne kasar ta Mali ta hanawa jirage da dama na rundunar MIMUSMA sauka da tashi daga kasar, har ma da jiragen leken asiri marasa matuka na drones.

Akalla dakarun kasar ta Jamus 1000 ne yanzu haka ke cikin rundunar tsaron ta MINUSMA a kasar Mali.

Tun bayan da Soji suka hambarar da mulkin farar hula a Mali cikin watan Agustan 2020, shugabancin kasar ya fara tsaurara alakar da ke tsakaninta da manyan kasashen Duniya musamman Faransa da ke matsayin uwar goyonta.

A makon da ya gabata ne a karon farko Sojin na Mali suka bayyana rufe iyakokin kasar ga kasashe kungiyar CEDEAO bayan da kungiyar ta dau wasu jerin takunkuman da suka hada da rufe kan iyakokinta ga Mali  da kuma rike kudaden kasar da ke bankin hadakar kungiyar kasashe masu amfani da Sefa na Eumoa da nufin hana sojojin ci gaba da kankame madafan ikon kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.