Dubban 'yan Burkina sun yi zanga-zangar goyon bayan juyin mulki
Magoya bayan sojojin da suka gudanar da juyin mulki a kasar Burkina Faso sun gudanar da zanga zangar nuna musu goyon baya kan kawar da zababbiyar gwamnatin kasar, a daidai lokacin da kungiyar kasashen Afirka ta Yamma da Majalisar Dinkin Duniya ke adawa da matakin.
Wallafawa ranar:
Daruruwan magoya bayan sojin ne suka shiga gangamin da aka yi a dandalin kasa da ke tsakiyar birnin Ouagadougou inda suke dauke da tutar kasar suke kuma busa sarewa da bayyana goyan bayan su ga shugabannin sojin.
Daya daga cikin masu shirya gangamin Lassane Ouedrago ya ce sun dade suna kira ga shugaban Christian March Kabore da ya sauka daga kujerarsa saboda gazawa wajen magance kashe kashen da ake yi a cikin kasar amma yaki.
A ranar Litinin, Jami’an sojin Burkina Faso suka kama shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore, wanda ya sha fuskantar zanga-zangar adawa daga dubban jama’a akan gazawarsa wajen dakile hare-haren ‘yan ta’adda a kasar.
A halin yanzu dai kasar da ke yankin Sahel tana karkashin kungiyar sojoji ‘yan Kishin Kasa ta MPSR, wadda Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba ke jagoranta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu