Isa ga babban shafi

Ana ci gaba da daga murya tsakanin Mali da Faransa

Wani jami'in gwamnatin majalisar sojin rikon kwaryar Mali ya bukaci ministan ayukan sojin Faransa, Florence Parly da ta rufe bakinta.

Wasu daga cikin yan  kasar Mali a birnin Bamako
Wasu daga cikin yan kasar Mali a birnin Bamako AFP - FLORENT VERGNES
Talla

A yau juma’a ministan harakokin wajen Faransa Jean Yves Ledrian daga nasa bangaren ya caccaki sojojin dake mulkin kasar ta Mali da cewa ba halataci bane da kuma ke daukar matakai na rashin sanin ciwon kai.

A daya bangaren Ministan harakokin wajen kasar ta Mali Abdoulaye Diop a wata hira da tashar talabijen na France 24,ya na mai cewa Mali kasa ce mai cin gashin kan ta, majalisar sojin kasar na a shirye don ganin ta shiga tattaunawa da kasar Faransa.

Ministan ya caccaki Jean Yves Ledrian da cewa Faransa ta daina katsan landan a harakokin ta na cikin gida.

Abdoulaye Diop, Ministan harakokin wajen Mali
Abdoulaye Diop, Ministan harakokin wajen Mali © RFI/France24

Abdoulaye Diop ya yi tir da kalaman shuwagabannin  kasashe a kan kasar Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.