Sojojin Algeria guda 2 sun mutu lokacin artabun da suka yi da ‘Yan ta’adda
Ma'aikatar tsaron Algeria ta sanar da cewar sojojin ta guda 2 sun mutu lokacin artabun da suka yi da ‘Yan ta’adda kusa da iyakar Nijar, yayin da suma suka kashe biyu daga cikin su.
Wallafawa ranar:
Sanarwar sojin ta ce anyi arangamar ce a yankin Hassi Tiririne dake kusa da Jamhuriyar Nijar. Sojojin Algeria na yawan bada irin wadannan sanarwar hallaka Yan ta’adda shekaru 20 bayan kawo karshen yakin basasar kasar wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane sama da 200,000.
Duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla a shekarar 2005 na kawo karshen tashin hankalin, Yan bindiga na ci gaba da kai hare hare akan jami’an tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu