Isa ga babban shafi
Algeria-Faransa

Le Drian na ziyara a Algeria don gyara alakar kasar da Faransa

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya isa Algeria a yau laraba, a wani yunkuri na gyara alakar kasashen biyu bayan sabanin da suka samu a baya-bayan nan wanda ya kai ga musayar janye jakadun juna.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian. SAFIN HAMED / AFP
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce Le Drian zai fara tattaunawa da takwaransa na Algeria Ramtane Lamamra gabanin ganawa da shugaba Abdelmadjid Tebboune.

Tuni dai ma’aikatar wajen Algeria ta sanar da ziyarar ta Le Drian a Algiers ko da ya ke bata bayyana takaimaiman batun da ganawar za ta mayar da hankali akai ba.

Alaka tsakanin Algeria da Faransa ta samu nakasu ne biyo bayan takun saka tsakanin gwamnati Tebboune da shugaba Emmanuel Macron dai dai lokacin da kasar ta Turai ke tsananin bukatar tsohuwar ‘yar goyon na ta a kokarin yakar matsalolin da suka addabi yankin Sahel.

Shugaba Emmanuel da kansa ya sake rura wutar rikicin bayan da ya kalubalanci Abdelmadjid Tebboune dangane da yadda ya ke tafiyar da mulkin kasar.

Kalaman na Macron dai ya sanya Tebboune kauracewa taron zaman lafiyar Libya cikin watan Nuwamba duk da kasancewar kasar ja gaba a kokarin yaki da matsalar da Libyan ke fuskanta.

Haka zalika Algeria ta fusata da matakin Faransa na rage yawan ‘yan kasar da za ta rika baiwa takardun Visa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.