Isa ga babban shafi
Mali - Faransa

Wata kungiyar Likitocin Faransa ta dakatar da aikin agaji a Mali saboda tsaro

Kungiyar agaji ta Medecins du Monde ta kasar Faransa ta sanar da shirin dakatar da tallafin jinkai ga dubban majiyyata a wasu yankuna biyu na arewa maso gabashin kasar Mali saboda tabarbarewar tsaro.

Sojojin hadin guiwar kasashen waje na musamman ta Tukuba dake Mali.
Sojojin hadin guiwar kasashen waje na musamman ta Tukuba dake Mali. Thomas COEX AFP
Talla

Shugaban kungiyar reshen Mali Giseppe Raffa, yace ayyukan mayaka masu ikirarin jihadi, da wasu kungiyoyi masu dauke da makamai na tasari matuka kai tsaya ga jami’an.

A shekarar da ta gabata wasu ‘yan bindiga sun kai hari daya daga cikin ma’aikatunta da kuma asibitin ta na tafi da gidanka a yankin Menaka, yayin da a farkon wannan watan aka yi garkuwa da wani ma’aikacinta a yankin Goa kafin daga bisani aka sake shi.

Jami’in ya ce kungiyar agajin ta yi imanin cewa masu aikata laifuka ne ke da laifi, kuma mai yiyuwa ne su yi amfani da “rashin tsaro” yayin da sojojin kasashen waje da na cikin gida da ke yaki da masu ikirarin jihadi ke kokarin sake fasalin yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.