Isa ga babban shafi
Mali

Mali ta amince a kai mata dakarun kiyaye zaman lafiya daga Chadi

Kasar Mali ta amince da karbar karin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dubu 1,000 daga kasar Chadi da ke makwabtaka da ita.

Assimi Goita, jagoran gwamnatin sojin Mali.
Assimi Goita, jagoran gwamnatin sojin Mali. © Nipah Dennis / AFP
Talla

Matakin Mali na amincewa da karin Dakarun wanzar da zaman lafiyar na MINUSMA, na kunshe ne cikin wasikar da jakadan Mali a zauren Majalisar Dinkin Duniya ya mikawa kwamitin sulhu.

Yarjejeniyar dai na zuwa ne a daidai lokacin da Faransa ke rage yawan dakarunta a kasar ta Mali, bayan da ta fara shiga tsakani a shekara ta 2013 domin fatattakar 'yan tayar da kayar baya.

A cikin watan Yuni, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da shirin na rage yawan sojojinsa da ke, bayan juyin mulkin farko na watan Agustan shekarar 2020 da Kanal Assimi Goita ya jagoranci yi, da ya kawo karshen gwamnatin tsohon shugaba Ibrahim Boubacar Keita.

Tuni dai Faransa ta rufe sansanoni uku a arewacin Mali a bana, yayin da take cigaba da shirin rufe sauran a nan gaba.

Tun cikin shekarar 2012, Mali ta fara fuskantar hare-haren masu tayar da kayar baya daga arewacinta, tashin hankali da daga bisani ya bazu zuwa makwaftanta da suka hada da Jamhuriyar Nijar da kuma Burkina Faso, lamarin da yayi sanadin mutuwar dubban mutane, wasu kusan miliyan biyu kuma suka rasa muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.