Isa ga babban shafi
MAROCO-CETO

Masu aikin ceto a Maroko na gab da ceto karamin yaro da ya fada rijiya .

Yanzu haka dai kasar Maroko na ci gaba da kokari a aikin da masu ceto  ke yi wajen ceto Rayan wani karamin yaro mai shekaru 5 a duniya daga hallaka bayan da ya fada cikin wata matsatsiyar  rijiya burtsatse mai zurfin mita 32, inda makomar rayuwarsa ke ci gaba da tada hankalin  mahukumtan masarauta ta Maroko da ke yankin arewacin nahiyar Afrika.

Masu aikin ceto a Maroco na kokarin ceto Rayan, wani karamin yaro  da ya fada rijiyar burtsatse.
Masu aikin ceto a Maroco na kokarin ceto Rayan, wani karamin yaro da ya fada rijiyar burtsatse. AFP - STR
Talla

Yanzu haka dai sannu a hankali ana ci gaba da aikin hakar ramen ceton a daura da rijiyar burtsatsen dake wani  kauye  dake yankin hamadar areawacin kasar ta Maroko.

 Mitaci biyu da suka rage a kai ga karamin yaro Rayan da ya fada rijiyar mai zurfin mita 32,  sun kasance masu wuyar haka,  sanadiyar hatsarin da ake iya fuskanta na ruftawar rijiyar burtsatsen baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.