Isa ga babban shafi

Sojin Burkina Faso za suyi mulkin shekaru 3 - Laftanar Kanar Damiba

Shugaban mulkin sojin Burkina Faso Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba ya sanya hannu akan shirin gwamnatin rikon kwaryar na shekaru 3 kafin gudanar da zabe, wata guda bayan juyin mulkin da suka yi a kasar.

Laftana Kanar  Paul-Henri Damiba, Shugaban majalisar sojin Burkina Faso
Laftana Kanar Paul-Henri Damiba, Shugaban majalisar sojin Burkina Faso via REUTERS - Burkina Faso Presidency Press Se
Talla

Sanarwar gwamnatin kasar tace sojojin zasu kwashe watanni 36 suna rike da mukaman mulki kafin gudanar da zaben da zasu mika mulki ga fararen hula.

Laftana Kanar Paul Henri Damiba Shugaban majalisar sojin Burkina Faso
Laftana Kanar Paul Henri Damiba Shugaban majalisar sojin Burkina Faso AFP - LEONARD BAZIE

Wannan adadi na watanni 36 ya saba na watanni 30 da majalisar bada shawara tayi a watan jiya.

Sanarwar tace daga cikin ayyukan da sojojin zasu mayar da hankali akai harda yaki da ta’addanci da kuma dawo da martabar kasar.

Tuni kungiyar ECOWAS da kungiyar kasashe Afrika ta AU suka dakatar da kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.