Isa ga babban shafi
Mali-Ta'addanci

Sojoji 27 sun mutu a harin ta'addancin Mali

 Rundunar sojn Mali  ta ce wani hari da mayaka masu ikirarin jihadi suka kai wani sansanin soji ya yi sanadin mutuwar jami’anta 27, a yayin da dakarunta suka kashe maharan 47.

Jagoran gwamnatin sojin Mali Kanar Assimi Goita.
Jagoran gwamnatin sojin Mali Kanar Assimi Goita. AFP - NIPAH DENNIS
Talla

Sojoji 33 ne suka jikkata a gumurzun, 21 daga cikinsu sun samu munanan raunuka, kana wasu 7 sun bace, kamar yadda rundunar sojin Mali din ta bayyana a wata sanarwa.

Kasar da ke yankin yammacin Afrika na fama da  matsalar hare-hare daga kungiyar IS mai nasaba da Al-Qaeda kusan shekaru 10 da suka wuce, inda kusan kashi 2 cikin 3 na kasar ke hannun ‘yan ta’addan.

Wata majiyar sojin Faransa da ta nemi a sakaya sunanta ta ce daruruwan mayaka masu ikirarin jihadi ne suka kai farmaki sansanin sojin mai kunshe da dakaru  kimanin 150 da misalin karfe 6  agogon  GMT, inda ta ce wadanda suka mutu sun za su kai 40 zuwa 50.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.