Isa ga babban shafi
Nijar

'Yan ta'adda sun kashe mutane 18 a kan iyakar Nijar da Mali

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce ‘yan ta’adda sun kashe mutane akalla 18, a wani farmaki da suka kai yankin yammacin kasar da yayi iyaka da Mali.

Sojojin Nijar na sintiri a yankin Ayoru da ke arewa maso yammacin kasar.
Sojojin Nijar na sintiri a yankin Ayoru da ke arewa maso yammacin kasar. © ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Bayanai sun ce an kai mummunan harin ne a ranar Lahadi, inda gungun maharan haye kan babura suka bude wuta kan wata babbar mota da ke safara tsakanin kauyukan Tillaberi, a yankin da ya hada iyakokin kasashen Burkina Faso, Mali da kuma Jamhuriyar ta Nijar.

Sanarwar ma’aikatar cikin gidan Nijar ta ce, adadin mutanen da kawo yanzu aka tabbatar da mutuwarsu 18 ne, wasu 8 suka jikkata, kuma biyar daga cikinsu na cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.

Ma’aikatar cikin gidan ta kara da cewar bayan budewa fasinjojin wuta, sai da ‘yan ta’addan suka kone babbar motar bayan sace dukiyar da ke cikinta, kuma a halin da ake ciki tuni jami’an tsaron Nijar suka kaddamar da farautar maharan.

Yankin Tillaberi dai ya sha fama da hare-haren ta’addanci, inda a ranar 2 ga watan Nuwamba a shekarar 2021, gungun mahara suka kashe jami’an tsaron sa-kai akalla 69.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.