Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

MDD ta tsawaita zaman dakarunta a Sudan ta Kudu

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar tsawaita aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu da shekara guda, kuri’ar da kasashen Rasha da China suka kauracewa.

Wsau sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu.
Wsau sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu. © Reuters /. Thomas Mukoya
Talla

Daukacin sauran mambobin kwamitin 13 duk sun amince da matakin na ci gaba da zaman rundunar wanzar da zaman lafiyar har zuwa ranar 15 ga watan Maris na badi.

Kasar Sin ta nuna goyon bayanta ga tsawaita wa'adin zaman rundunar, amma ta zabi kauracewa zaben saboda Amurka ta dage kan shigar da batun kare hakkin dan Adam a cikin daftarin kudurin.

Kimanin sojoji dubu 17 ne karkashin Majalisar Dinkin Duniya da kuma ‘yan sanda dubu 2 da 100 ke aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu.

Aikin dai na daya daga cikin mafi tsada ga Majalisar Dinkin Duniya, inda kasafin kudin shekara na tafiyar da rundunar ya zarce dala biliyan daya.

Wani sojan Majalisar Dinkin Duniya yayin sintiri a birnin Juba.
Wani sojan Majalisar Dinkin Duniya yayin sintiri a birnin Juba. © UN Photo/Isaac Billy

A wani taron komitin sulhu da aka yi a farkon watan Maris, Majalisar Dinkin Duniya da Amurka, wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen samar da kasar Sudan ta Kudu, sun bukaci shugabanninta da su ci gaggauta shirya gudanar da zabuka ko kuma su fuskanci wani bala'i.

Yayin da ya rage kasa da shekara guda a gudanar da zabe, cikin watan Fabarairun da ya gabata Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin Sudan ta Kudu na iya fuskantar barazanar sake fadawa cikin yaki.

Kasa mafi karancin shekaru a duniya ta fuskanci rashin zaman lafiya tun bayan samun 'yancin kai daga Sudan a shekara ta 2011, inda a tsakanin shekara ta 2013 zuwa 2018, ta fada cikin yakin basasa tsakanin sojoji mabiya Riek Machar da shugaban kasar Salva Kiir, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 400,000 tare da raba miliyoyi.

Yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a shekarar 2018 ta kai ga kafa gwamnatin hadin kan kasa da aka kaddamar a watan Fabrairun shekarar 2020, inda Kiir ya zama shugaban kasa da kuma Machar a matsayin mataimakin shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.