Isa ga babban shafi
TUNISIA - ta'addanci

Ana zargin 'Yan ta'adda ta kai hari a ofishin 'yan sandan Tunisiya

Rundunar ‘Yan sandan Tunisia ta ce an yi musayar wuta tsakanin wasu da ake zargin mayaka masu ikirarin jihadi ne da ‘yan sanda a kusa da wani barikin jami’an tsaron kasa da sanyin safiyar Lahadi a yankin Kairouan da ke tsakiyar kasar.

'Yan sandan Tunisia yayin zanga-zangar adawa da shugaban kasar Kais Saied a Tunis, 10/10/2021.
'Yan sandan Tunisia yayin zanga-zangar adawa da shugaban kasar Kais Saied a Tunis, 10/10/2021. Copyright 2021 The Associated Press. All rights reserved.
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar ‘yan sandan Tunisia tace ‘yan bindigar da ke cikin wata mota sun bude wuta, amma jami’an tsaro sun maida martani nan dake tare da dakile yunkurin ba tare da samun asarar rai ba.

Harin dai ya zo ne a ranar da kasar ke bukin samun ‘yancin kai daga Faransa, kuma kasar ta fada cikin rikicin siyasa tun bayan da shugaba Kais Sa’id ya kwace mulki a watan Yulin da ya gabata.

Bayan juyin juya hali na shekara ta 2011 da ya hambarar da shugaba Zine El Abidine Ben Ali da ya dade yana mulkin kasar, Tunisiya ta fuskanci yawaitar hare-haren 'yan bindiga a fadin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.