Isa ga babban shafi
Mali - Ta'addanci

Dakarun Mali sun kashe 'yan ta'adda 203

Sojin Mali  ta ce ta kashe mayaka 203 a wani samame da ta kai a wasu yankunan kasar, lamarin da ke nuni da karuwar ba ta kashi tsakanin dakarun gwamnati da kungiyoyi masu ikirarin jihadi a kasar da yaki ya daidaita.

Sojojin Mali yayin atsaye a yankin Mopti dake tsakiyar Kamaru.
Sojojin Mali yayin atsaye a yankin Mopti dake tsakiyar Kamaru. AP - Francois Rihouay
Talla

Rundunar sojin ta ce ta kai  samamen ne a tsakanin 23 zuwa 31 ga watan Maris a garin Moura na yankin Sahel, inda ta bayyana a matsayin wata tunga ta ‘yan ta’adda.

A cewar wata sanarwa daga rundunar sojin ta Mali, dakarun gwamnati sun kashe mayaka 203, suka kuma kama 51, tare da kwace dimbim makamai.

Sanarwar na zuwa ne  bayan rahotannin da suka karade kafafen sadarwar zamani a wannan makon  cewa an kashe gwamman mutane, ciki har da fararen hula a yankin Moura.

Sai dai kamfanin dillancin labaran Faransa ta ce har yanzu ba ta kai ga tantance sahihancin rahotannin biyu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.